Ilimi Hasken Rayuwa

Kalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - kashi na 2

Informações:

Sinopsis

Shirin na yau, ya ɗora ne akan kashi na farko da muka gabatar a makon jiya, wanda ya yi duba game da yadda harshen Hausa ya bunkasa a lokutan baya, da muhimmacinsa, baya ga matsalolin da yake fuskanta da ma kalubalen da Rubutun Hausa ke fuskanta a kafofin sada zumunta.  Masana sun bayyana ka'idojin rubutun Hausa, a matsayin wani yanayi na lura tare da kiyaye ka'idojin harshen Hausa a rubuce domin samun damar isar da sakon da marubuci ke nufi zuwa ga mai karatu daidai ba tare da dungushe ko sauya ma'anar da marubuci ke nufi ba. A cewar masanan kiyaye ƙa'idodin rubutun yana kuma samar da saukin fahimtar karatu daga mai karantawa.Ko da a kafafen yada labarai, rashin kiyaye ka'idojin rubutun Hausa yakan taka rawa wajen sauya ma'anar labari, to ko ya masu bibiyar shafukan  yanar gizo na kafafen watsa labarai ke ji idan suka ga ba a yi amfani da harufa masu lanƙwasa ba kamar Ɓ da Ɗ da kuma Ƙ? Ga abinda wasu ke cewa.