Lafiya Jari Ce

Yadda cuɗanya wajen amfani da moɗa ko cokali ke taimakawa wajen yaɗa cutuka

Informações:

Sinopsis

Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon, ya mayar da hankali ne kan nau’ikan cutukan da ke bazuwa sakamakon cuɗanyar da jama’a ke yi wajen amfani da kayayyakin da bisa ƙa’ida yakamata kowanne mutum ya yi amfani da nasa shi kaɗai. Har yanzu ana samun waɗanda ke yin gamayya wajen amfani da moɗar-shan ruwa ko cokali ko kuma kwanon cin abinci dama sauran kayakin da basu cancanci amfanin gamayya ba, lura da yadda cikin sauƙi hakan ke iya yaɗa cutuka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........