Kasuwanci

Yadda manoman zoɓo a Najeriya suka  fuskanci kalubale a harkar

Informações:

Sinopsis

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya mayar da hankali ne kan halin da ake ciki game da noman zoɓo a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, da kuma yadda ake fita da shi zuwa ƙasashen ƙetare. Duk da cewa ana noman zoɓo a Jihohi irin su Zamfara da Katsina da Kano da Kebbi da Borno da Yobe, bayanai na cewa kusan kaso 70 cikin 100 na zobon da ake fita da shi ƙasashen waje a jihar Jigawa ake nomawa, sai dai a shekaru biyu da suka gabata manoman na zoɓo sun ɗan  fuskanci kalubale a harkar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..........