Lafiya Jari Ce

Annobar ƙyanda ta tilastawa mahukunta Nijar yin rigakafin ƙasa baki ɗaya

Informações:

Sinopsis

Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan shaushawar ƙyandar da mahukuntan Jamhuriyar Nijar suka jagoranta sakamakon ɓullar cutar wadda a duk lokacin da aka ga bazuwarta ta ke yiwa ƙananan yara illa matuƙa. Dai dai lokacin da duniya ta gudanar bikin makon rigakafi a ƙarshen watan Mayun da ya gabata, a Jamhuriyyar Nijar annobar ƙyanda ce ke ci gaba da yaɗuwa tare da galabaitar da ɗimbin ƙananan yara, lamarin da ya tilasta mahukunta ɗaukar matakan yiwa jama’a rigakafin wannan cuta mai haɗari.Cutar ta Ƙyanda ko Ado ko kuma Dusa na matsayin babbar matsalar kiwon lafiya ta yadda a duk lokacin da ta ɓulla ta kan haddasa asarar ɗimbin rayuka, kodayake a yanzu tuni ma’aikatar lafiya ta jagoranci aikin rigakafin na ƙasa baki ɗaya da zai shafi dukkanin ƙananan yara tun daga watanni 6 da haihuwa har zuwa shekarun 5 da nufin murƙushe cutar.Tsawon mako guda aka shafe daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Mayu ana gudanar da rigakafin na ƙyanda a sassan Nijar wanda aka yiwa ƙananan y