Wasanni

Yadda shugaban Najeriya ya tarbi tawagar Super Falcons bayan lashe gasar WAFCON

Informações:

Sinopsis

Shirin a wannan makon zayyi duba ne kan karramawar da gwamnatin Najeriya ta yi wa tawagar Super Falcons na lashe gasar WAFCON. A makon da ta gabata ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karrama ƴan wasan tawagar ƙungiyar kwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Falcons, bayan nasarar lashe kofin WAFCON karo na 10 daga cikin 13 da aka yi. Cikin kyautukan da gwamnati ta baiwa waɗannan ƴan wasa akwai lambar girmamawa na ƙasa wato OON da shugaban Tinubu ya baiwa dukkan ƴan wasan da masu horar dasu, hakazalika kowacce ƴar wasa ta samu dalan amurka dubu 100, da kuma karin naira miliyan goma-goma daga ƙungiyar gwamnonin Najeriya. Tuni dai shugaban hukumar wasani a Najeriya Shehu Dikko ya yaba da wannan nasarar da kuma irin karramawar da shugaban ƙasar ya yiwa ƴan wasan. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.