Wasanni
Yadda wasannin sharen fagen zuwa gasar cin kofin duniya ke gudana a Afrika
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:10:00
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Kawo yanzu dai wasanni sun ɗauki zafi ganin cewa wasu daga cikin tawagogin ƙasashen sun fara jin kanshin halartar gasar, amma kuma wasu har yanzu tana ƙasa tana dabo. Tawagar ƙasar Morocco tuni ta samu nata tikitin bayan da ta haɗa maki 18, tazarar maki 8 tsakaninta da Tanzania. Tawagogin ƙasashe irinsu Masar da Algeria da Tunisia da Ghana da Afrika ta Kudu, duk da cewa akwai tazarar maki masu ɗan dama tsakaninsu da waɗanda ke mataki na biyu a rukunansu, har yanzu akwai sauran rina a kaba.