Lafiya Jari Ce

Yadda yakamata a tunƙari cutukan da ke yawaita a lokacin damuna

Informações:

Sinopsis

Shirin na Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda ake ganin yawaitar jinyace-jinyace mabanbanta da kan kwantar da jama’a kama daga mashasshara ko mura ko kuma ƙurajen jiki dama wasu nau’in cutukan daban-daban, musamman ga ƙananan yara a lokacin damuna. Zubar ruwan sama da yawaitar ƙwari baya ga raɓa na daga cikin abubuwan da kan haddasa cutukan dama ƙamjiki, batun da Dokta Ila Aishatou jagorar gidan asibiti CSI stade a birnin Damagaram ke cewa akwai matakai na kare kai daga irin cutukan na damuna musamman ga ƙananan yara. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.