Al'adun Gargajiya

Yadda aka bar baya da ƙura a girmamawar da ka yiwa Rarara da digirin Dakta

Informações:

Sinopsis

Shirin Al’adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la’akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen. Tun cikin makon jiya masana da sauran jama’ar gari ke tofa albarkacin bakunansu akan karramawar  da wata Jami’a mai suna European-American University ta yi wa fitaccen mawaƙin siyasa a Najeriya Dauda Kahutu Rarara, wanda ta bai wa Digirin Girmamawa na Dakta. Reshen Jami’ar da bayanai a yanar gizo suka nuna cewar hedikwatarta na ƙasar Faransa ne ta yi bikin Karrama mawaƙi Raran ne a Abuja, ranar Asabar, 20 ga watan nan na Satumba, taron da ya samu halartar wasu fitattun mutane. Sai dai Kash! ‘yan sa’o’i bayan bikin da aka yi Jami’ar da ake alaƙanta da Turai da Amurka ta ce ba ta fa san zance ba, domin ba da yawunta aka miƙa wa fitaccen mawaƙin siyasar Digirin na Girmamawa ba, zalika dukkanin mutanen da suka yi iƙirarin alaƙanta kansu da ita ta barranta da su, domin sun yau