Bakonmu A Yau
Tattaunawa kan umarnin Tinubu ga ministocinsa na arewa don tallata ayyukansa
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:03:35
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
A Najeriya rahotanni sun bayyana cewar yanzu haka shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkanin ministocinsa da suka fito daga yankin arewacin ƙasar su koma jihohin da suka fito domin kare manufofinsa da kuma bayyana irin ayyukan da yake yi. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban ke ganin matsananciyar suka daga ɓangaren adawa da kuma ganin tarin barazana musamman kan salon kamun ludayin gwamnatinsa.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Harsanu Yunusa Guyaba.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.