Bakonmu A Yau

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 1:20:18
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Emmanuel Macron kan amincewa da ƙasar Falasɗinu da kuma yakin Ukraine da Rasha

    25/09/2025 Duración: 03min

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasar Rasha ta yi rauni sosai a yaƙin da take gwabzawa da Ukraine. Macron ya bayyana haka ne a zantawa ta musamman da ya yi tashar talabijin ta France24 da Kuma RFI a gefen Babban Taron Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York, inda ya taɓo batutuwa da dama ciki har da amincewa da Palesdinu a matsayin ƙasa da daidai sauransu. Da farko dai Emmanuel Macron ya jinjina wa shugaba Amurka Donald Trump ne a game da ƙoƙarinsa don kawo ƙarshen rikicin Ukraine. Ku latsa alamar sauti don sauraron fassarar kalamansa...............

  • Maitre Lirwanou Abdourahman kan ficewar Nijar Mali da Burkina Faso daga ICC

    24/09/2025 Duración: 03min

    Burkina Faso, Mali da kuma Nijar sun sanar da janyewar ƙasashensu daga Kotun Hukunta Laifufuka ta Duniya da ke birnin Hague. A sanarwar haɗin-gwiwa da suka fitar cikin daren litinin da ta gabata, ƙasashen uku sun ce sun ɗauki matakin saboda sun lura cewa kotun ta rikiɗe domin zama ƴar amashin ƴan mulkin mallaka. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani dokokin ƙasa da ƙasa Maitre Lirwanou Abdourahman, domin jin ko wataƙila ya yarda da dalilan da wadannan ƙasashe suka gabatar. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.

  • Maitre Lirwanou Abdourahman kan janyewar ƙasashen AES daga kotun ICC

    24/09/2025 Duración: 03min

    Burkina Faso da Mali da kuma Nijar sun sanar da janyewar ƙasashensu daga Kotun Hukunta Laifufuka ta Duniya da ke birnin Hague. A sanarwar haɗin-gwiwa da suka fitar cikin daren Litinin da ta gabata, ƙasashen uku sun ce sun ɗauki matakin ne saboda sun lura cewa kotun ta rikiɗe domin zama ƴar amashin ƴan mulkin mallaka. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani dokokin ƙasa da ƙasa Maitre Lirwanou Abdourahman, domin jin ko wataƙila ya yarda da dalilan da wadannan ƙasashe suka gabatar. Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawarsu.................

  • Farfesa Tukur Abdulƙadir kan ƙarin ƙasashen da ke amincewa da Falasɗinu

    23/09/2025 Duración: 03min

    Ƙasashen duniya na ci gaba da nuna amincewarsu da samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu, a wata guguwa wadda ba’a taɓa ganin irinta ba. Ƙasashen turai da ake ganin suna da ƙyakyawar alaƙa da Amurka irinsu su Burtaniya, Canada da kuma Australia a wannan Karo sun sanar da amincewar su da baiwa Falasɗinu damar zama ƙasa mai cin gashin kanta amma bisa wasu shariɗoɗi. A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce har yanzu da sauran rina a kaba don kuwa amincewar waɗannan ƙasashe ƙadai a fatar baki bata wadatar ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

  • Tattaunawa da tsohon Jakadan Kamaru Ambasada Malam Mohamed Sani kan zaɓen ƙasar

    22/09/2025 Duración: 03min

    A ƙarshen wannan mako ne za a ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru, zaɓen da zai gudana a ranar 12 ga watan gobe na Oktoba. To sai dai yayin da jam’iyyar RDPC mai mulki ta bayyana Paul Biya a matsayin wanda zai tsaya mata takara, a nasu ɓangare kuwa, yanzu haka ƴan adawa, na ci gaba da tattaunawa don fitar da mutum ɗaya da zai tsaya zaɓen amadadinsu. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ambasada Malam Mohamed Sani, tsohon jakada a lokacin mulkin Ahmadou Ahidjo, amma a yanzu yake zaune a ƙetare, inda ya bayyana yadda suke kallon wannan zaɓe.

  • Ambasada Mohamed Sani kan zaɓen shugaban ƙasa da za a yi a Kamaru

    22/09/2025 Duración: 03min

    A ƙarshen wannan mako ne za a ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar 12 ga watan gobe na Oktoba idan Allah ya kai mu a Kamaru. To sai dai yayin da jam’iyyar RDPC mai mulki ta bayyana Paul Biya a matsayin wanda zai tsaya mata takara, a nasu ɓangare kuwa, yanzu haka ƴan adawa, na ci gaba da tattaunawa don fitar da mutum ɗaya da zai tsaya musu takara a zaɓen. Kan haka Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ambasada Malam Mohamed Sani, tsohon jakada a lokacin mulkin Ahmadou Ahidjo, amma a yanzu yake zaune a ƙetare, inda ya bayyana yadda suke kallon wannan zaɓe. Ƙu latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............

  • Shugabannin ƙananan hukumomin Kwara sun sanar da rufe kasuwannin sayar da shanu

    19/09/2025 Duración: 03min

    Shugabannin ƙananan hukumomi a yankin Kudancin jihar Kwara ta Najeriya sun sanar da rufe dukkannin kasuwannin sayar da shanu da aka fi sani da {Kara}. Mahukuntan sun ce sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon tashin matsalolin tsaro da ake samu a kasuwannin. A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara shugaban ƙungiyar Miyetti Allah reshen jihar ta kwara, kuma guda daga cikin jagororin ƙungiyar kasuwannin kara na jihar Alhaji Shehu Garba ya ce sam basu yarda da wannan mataki ba. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar tasu....

  • Hira da Issa Tchiroma Bakary game da zaɓen Kamaru da ƙoƙarin kawar da Paul Biya

    18/09/2025 Duración: 03min

    Issa Tchiroma Bakary, wanda ya share tsohon shekaru 16 yana riƙe da muƙamin minista ƙarƙashin gwamnatin Paul Biya na Kamaru, a yanzu ya koma ɓangaren adawa inda yake ci gaba da jawarcin sauran ƴan siyasa na ƙasar. Tuni dai wani ƙawance da ya ƙunshi jam’iyyin adawa 11 ya bayyana goyon baya ga takararsa a zaɓen shugabancin ƙasar da za a yi ranar 12 ga watan gobe idan Allah ya kai mu. Radio France Internationale ya zanta da tsohon minista Issa Tchiroma, wanda da farko ya bayyana matsayinsa dangane da wannan goyon baya da ya samu, inda ya ci gaba da cewa.

  • Dr. Musa Adamu game da yadda rashawa ke ci gaba da haɓaka a Najeriya

    17/09/2025 Duración: 03min

    Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nigeria wato ICPC, ta bayyana damuwa kan yadda matsalar rashawa ke ci gaba da haɓaka, duk kuwa da matakan da ta ke ɗauka. A cewar Shugaban hukumar ta ICPC, Dr Musa Adamu Aliyu, a yanzu sun karkata akalarsu ne zuwa ga ƙananan hukumomi, don daƙile matsalar cin hanci da ta yi katutu... Latsa alamar sauti don sauraron ƙarin bayanin da Dr Musa Adamu, ya yi wa wakilinmu Ibrahim Malam Goje........

  • Isa Tafida Mafindi-Kan yadda talakawa zasu mori raba fetur da Ɗangote ya fara da motocinsa

    16/09/2025 Duración: 03min

    Kamfanin Dangote ya fara aikin rarraba man fetur daga matatarsa zuwa sassan Najeriya domin saukakawa jama'a, a dai-dai lokacin da manyan dilallan man fetur ke adawa da matakin. Dashi Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Alahji Isa Tafida Mafindi a kan yadda talakawa zasu ci gajiyar wannan shirin. Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar.

  • Uzairu Abdullahi kan buƙatun likitocin Najeriya masu neman ƙwarewa ga gwamnati

    15/09/2025 Duración: 03min

    A makon da ya gabata ne likitoci da ke neman ƙawarewa a Najeriya suka gudanar da yajin aiki, domin nuna rashin amincewa dangane da yadda gwamnati ke jan ƙafa wajen ƙin biyansu haƙƙoƙinsu.To sai dai bayan da aka fara biyansu wasu daga cikin haƙƙoƙin, sun dakatar da yajin aikin tare da bai wa gwamnati ƙarin makonni biyu domin shafe musu hawayensu. Dr Uzairu Abdullahi, shi ne Editan Mujallar wallafa labarai ta ƙungiyar ya yi ƙarin bayani..... Latsa alamar sauti domin sauraron tattaunawar da Abdoulkarim Ibrahim Shikal........

  • Dr Mubarak Muhammad kan naɗin sabon firaministan Faransa Lecornu

    11/09/2025 Duración: 03min

    Sabon firaministan Faransa Sebastien Lecornu ya karɓi ragamar tafiyar da mulkin daga hannun Francois Bayrou, wanda ƴan Majalisar dokokin ƙasar suka tsige a ranar Litinin ta gabata.Wannan dai shi ne Firaminista na 5 bayan da Emmanuel Macron ya karɓi ragamar mulki domin yin wa’adi na biyu, lamarin da ke nuni da cewa ƙasar na fama da rikici a fagen siyasa. Dr Mubarak Muhammad, mazauni Faransa kuma masani a game da salon siyasar ƙasar, ya bayyana wa Nura Ado Sulaiman mahangarsa a game da wannan batu. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu..................

  • Mammane Wada kan yadda jamhuriyar Nijar ke ci gaba da shaƙe wuyan masu chachakarta

    10/09/2025 Duración: 03min

    Gwamnatin mulkin sojin  Jamhuriyyar Nijar na ci gaba da kamen waɗanda ke sukar lamirinta da suka hadar da ƴan jarida da masu fafutuka har ma da ƴan siyasa. A wani rahoto da ta fitar a baya bayan nan kungiyar kare hakkin bil Adam Human Right Watch ta soki yadda sojojin da suka kwace muki a ƙasar ke tsare jama’a babu gaira babu dalili. Akan wanan abokin aiki Oumarou Sani ya tattaunawa da Mamane Wada shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.

  • Mamane Wada akan yadda Gwamnatin sojin Nijar ke kama waɗanda ke sukar lamirinta

    10/09/2025 Duración: 03min

    Gwamnatin mulkin sojin  Jamhuriyyar Nijar na ci gaba da kamen waɗanda ke sukar lamirinta da suka haɗar da ƴan jarida da masu fafutuka har ma da ƴan siyasa. A wani rahoto da ta fitar a baya bayan nan kungiyar kare haƙƙin bil Adam Human Right Watch ta soki yadda sojojin da suka ƙwace muki a ƙasar ke tsare jama’a babu gaira babu dalili. Akan wanan abokin aiki Oumarou Sani ya tattaunawa da Mamane Wada shugaban ƙungiyar yaƙi da cin hanci da rashawa ga kuma yadda zantawarsu ta gudana. Latsa alaamar sauti don sauraron yadda tattaunawar ta su ta gudana...........

  • Nasiru Garba Ɗantiye kan ƙorafin shugaban majalisar wakilan Najeriya game da yawan ciwo bashi

    09/09/2025 Duración: 03min

    Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Abbas Tajudeen, ya koka akan yadda bashi ya ke cigaba da yi wa ƙasar katutu, lamarin da ya ce yana barazana ga bunƙasar tattalin arziƙinta. Tajuddeen, wanda ya bayyana haka jiya Litinin a Abuja, ya ce bashin da ke kan Najeriya a yanzu ya kai wani matsayi mai ban tsoro, inda ya ke kira da a sake fasalin yadda ake karɓar rance a ƙasar. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da wani tsohon ɗan majalisar dokoki a ƙasar, Nasiru Garba Ɗantiye, ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.

  • Alhaji Dayyabu Garga akan batun fara yajin aikin ƙungiyar NUPENG a Najeriya

    08/09/2025 Duración: 03min

    A wannan litinin, ƙungiyar NUPENG da ta haɗa direbobin motocin dakon mai da iskar gas a Najeriya ta fara yajin aiki, domin nuna rashin amincewa da yadda Ɗangote ke shirin yin amfani da motocinsa domin rarraba man fetur a sassan ƙasar. Shugabannin NUPENG, sun ce su ne ke da hurumin raba mai da kuma iskar gaz a Najeriya, a maimakon yadda Ɗangote ke shirin yin amfani da motoci dubu huɗu domin wannan aiki. Latsa alamar sauti domin sauraro.......

  • Nijar a duk kullum za ta kare hakokin ƴan ƙasar mazauna ketare

    06/09/2025 Duración: 03min

    Jamhuriyar Nijar a duk kullum za ta kare hakokin ƴan ƙasar mazauna ketare, Wasu daga ciki tarin matsalolli da ƴan Nijar mazauna ƙasashen ketare ke fuskanta sun hada da rashin takardun zama wadanan kasashe. Jakadan Nijar a Jamhuriyar Benin, Kadade Chaibou ya bayyana haka yayin zantawa da Abdoulaye Issa a ofishinsa dake birnin Kwatanu.

  • Tattaunawa da Barr Al-Zubair kan jinkiri wajen gudanar da shara'o'i a Najeriya

    03/09/2025 Duración: 03min

    Masu ruwa da tsaki kan sha’anin Shari’a a Najeriya sun sabunta ƙorafin da suke yi a kan matsalar jinkiri maras tushe, wajen gudanar da shara’o’i ko yanke hukunci kan waɗanda ake tuhuma da aikata manyan laifuka, musamman na ta’addanci. Ƙorafin ya sake bijirowa ne la’akari da yadda cikin ƙanƙanin lokaci mahukuntan ƙasar Finland suka zartas da hukunci kan Simon Ekpa, wani mai iƙirarin neman kafa ƙasar Biafra a Najeriya. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hirar....

  • Muhammad Magaji kan ƙorafin manoma game da jinkirin raba kayayyyakin noma

    02/09/2025 Duración: 03min

    Manoma a Najeriya na kokawa kan ƙarancin samun taimako daga gwamnati wajen sauƙaƙa musu ayyukan noma. Ƙorafi na baya bayan nan a Najeriyar shi ne jinkirin raba wasu kayayyakin noma ciki har da motocin Tantan aƙalla dubu biyu da gwamnatin Najeriyar ta sanar da sayowa yau fiye da watanni biyu, yayin da a gefe guda tuni daminar bana ta yi nisa. Kan wannan al’amari Nura Ado Suleiman ya tattauna da Alhaji Muhd Magaji, Sakataren tsare tsare na ƙungiyar manoman Najeriya.

  • Fatima Baba Fugu akan 'yan Najeriya fiye da dubu 24 da suka ɓata

    01/09/2025 Duración: 03min

    Ƙuniyar Agaji ta Red Cross ta ce yanzu haka akwai mutane sama da dubu 23 da suka ɓata a sassan Najeriya. A bayanin da ta fitar a jiya lahadi, ƙungiyar ta ce 68% na waɗanda suka ɓata dukanninsu mata ne, yayin da jihar Yobe ke matsayin jagora ta fannin yawan waɗanda lamarin ya fi shafa. Fatima Baba Fugu, tana aiki ne da sashen da ke haɗa waɗanda suka ɓata da iyalansu a ƙungiyar ta ICRC daga birnin Maiduguri jihar Borno, ta yi wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal ƙarin bayani a game da waɗannan alkaluma da ƙungiyar ta fitar.

página 1 de 2