Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Alhaji Abubakar Maigandi kan tasirin daina sayarwa Ɗangote man fetur da Naira
02/04/2025 Duración: 03minGidajen man fetur a Najeriya na ci gaba da sauya farashi, bayan da matatar Dangote ta sanar da cewa yarjejeniyar da ke tsakaninta da NNPC wadda ke bayar da damar samun gurbataccen mai a farashin Naira ta kawo ƙarshe ba tare da an sabunta ta ba. Alhaji Abubakar Maigandi, shugaban ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya wato IPAM, ya ce tuni suka yi hasashen faruwar hakan bayan rugujewar waccan yarjejeniyar.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.
-
Barista Abba Hikima kan tsarin kiranye ga ƴan majalisu a dokokin Najeriya
27/03/2025 Duración: 03minA farkon makon nan, Hukumar Zaɓen Najeriya INEC, ta ce ba a kammala cika ƙa'idojin da kundin tsarin mulki ya gindaya ba, a kan tsarin kiranyen da ake ƙoƙarin yi wa Sanata Natasha mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattijai. INEC ta bayyana haka ne, bayan da ta fara nazari akan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar mata na nemn yi wa Sanata Natasha yankan ƙauna, wadda a kwanakin baya ta zargi shugaban Majalisar Dattawan Najeriyar Godswil Akpabio da cin zarafinta ta hanyar nemanta da lalata.Domin jin yadda tsarin na Kiranyen yake...Nura Ado Suleiman ya tattauna da Barista Abba Hikima, ƙwararren lauya a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.