Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Dr Mubarak Muhammad kan naɗin sabon firaministan Faransa Lecornu
11/09/2025 Duración: 03minSabon firaministan Faransa Sebastien Lecornu ya karɓi ragamar tafiyar da mulkin daga hannun Francois Bayrou, wanda ƴan Majalisar dokokin ƙasar suka tsige a ranar Litinin ta gabata.Wannan dai shi ne Firaminista na 5 bayan da Emmanuel Macron ya karɓi ragamar mulki domin yin wa’adi na biyu, lamarin da ke nuni da cewa ƙasar na fama da rikici a fagen siyasa. Dr Mubarak Muhammad, mazauni Faransa kuma masani a game da salon siyasar ƙasar, ya bayyana wa Nura Ado Sulaiman mahangarsa a game da wannan batu. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu..................
-
Mammane Wada kan yadda jamhuriyar Nijar ke ci gaba da shaƙe wuyan masu chachakarta
10/09/2025 Duración: 03minGwamnatin mulkin sojin Jamhuriyyar Nijar na ci gaba da kamen waɗanda ke sukar lamirinta da suka hadar da ƴan jarida da masu fafutuka har ma da ƴan siyasa. A wani rahoto da ta fitar a baya bayan nan kungiyar kare hakkin bil Adam Human Right Watch ta soki yadda sojojin da suka kwace muki a ƙasar ke tsare jama’a babu gaira babu dalili. Akan wanan abokin aiki Oumarou Sani ya tattaunawa da Mamane Wada shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.
-
Mamane Wada akan yadda Gwamnatin sojin Nijar ke kama waɗanda ke sukar lamirinta
10/09/2025 Duración: 03minGwamnatin mulkin sojin Jamhuriyyar Nijar na ci gaba da kamen waɗanda ke sukar lamirinta da suka haɗar da ƴan jarida da masu fafutuka har ma da ƴan siyasa. A wani rahoto da ta fitar a baya bayan nan kungiyar kare haƙƙin bil Adam Human Right Watch ta soki yadda sojojin da suka ƙwace muki a ƙasar ke tsare jama’a babu gaira babu dalili. Akan wanan abokin aiki Oumarou Sani ya tattaunawa da Mamane Wada shugaban ƙungiyar yaƙi da cin hanci da rashawa ga kuma yadda zantawarsu ta gudana. Latsa alaamar sauti don sauraron yadda tattaunawar ta su ta gudana...........
-
Nasiru Garba Ɗantiye kan ƙorafin shugaban majalisar wakilan Najeriya game da yawan ciwo bashi
09/09/2025 Duración: 03minKakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Abbas Tajudeen, ya koka akan yadda bashi ya ke cigaba da yi wa ƙasar katutu, lamarin da ya ce yana barazana ga bunƙasar tattalin arziƙinta. Tajuddeen, wanda ya bayyana haka jiya Litinin a Abuja, ya ce bashin da ke kan Najeriya a yanzu ya kai wani matsayi mai ban tsoro, inda ya ke kira da a sake fasalin yadda ake karɓar rance a ƙasar. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da wani tsohon ɗan majalisar dokoki a ƙasar, Nasiru Garba Ɗantiye, ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.
-
Alhaji Dayyabu Garga akan batun fara yajin aikin ƙungiyar NUPENG a Najeriya
08/09/2025 Duración: 03minA wannan litinin, ƙungiyar NUPENG da ta haɗa direbobin motocin dakon mai da iskar gas a Najeriya ta fara yajin aiki, domin nuna rashin amincewa da yadda Ɗangote ke shirin yin amfani da motocinsa domin rarraba man fetur a sassan ƙasar. Shugabannin NUPENG, sun ce su ne ke da hurumin raba mai da kuma iskar gaz a Najeriya, a maimakon yadda Ɗangote ke shirin yin amfani da motoci dubu huɗu domin wannan aiki. Latsa alamar sauti domin sauraro.......
-
Nijar a duk kullum za ta kare hakokin ƴan ƙasar mazauna ketare
06/09/2025 Duración: 03minJamhuriyar Nijar a duk kullum za ta kare hakokin ƴan ƙasar mazauna ketare, Wasu daga ciki tarin matsalolli da ƴan Nijar mazauna ƙasashen ketare ke fuskanta sun hada da rashin takardun zama wadanan kasashe. Jakadan Nijar a Jamhuriyar Benin, Kadade Chaibou ya bayyana haka yayin zantawa da Abdoulaye Issa a ofishinsa dake birnin Kwatanu.
-
Tattaunawa da Barr Al-Zubair kan jinkiri wajen gudanar da shara'o'i a Najeriya
03/09/2025 Duración: 03minMasu ruwa da tsaki kan sha’anin Shari’a a Najeriya sun sabunta ƙorafin da suke yi a kan matsalar jinkiri maras tushe, wajen gudanar da shara’o’i ko yanke hukunci kan waɗanda ake tuhuma da aikata manyan laifuka, musamman na ta’addanci. Ƙorafin ya sake bijirowa ne la’akari da yadda cikin ƙanƙanin lokaci mahukuntan ƙasar Finland suka zartas da hukunci kan Simon Ekpa, wani mai iƙirarin neman kafa ƙasar Biafra a Najeriya. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hirar....
-
Muhammad Magaji kan ƙorafin manoma game da jinkirin raba kayayyyakin noma
02/09/2025 Duración: 03minManoma a Najeriya na kokawa kan ƙarancin samun taimako daga gwamnati wajen sauƙaƙa musu ayyukan noma. Ƙorafi na baya bayan nan a Najeriyar shi ne jinkirin raba wasu kayayyakin noma ciki har da motocin Tantan aƙalla dubu biyu da gwamnatin Najeriyar ta sanar da sayowa yau fiye da watanni biyu, yayin da a gefe guda tuni daminar bana ta yi nisa. Kan wannan al’amari Nura Ado Suleiman ya tattauna da Alhaji Muhd Magaji, Sakataren tsare tsare na ƙungiyar manoman Najeriya.
-
Fatima Baba Fugu akan 'yan Najeriya fiye da dubu 24 da suka ɓata
01/09/2025 Duración: 03minƘuniyar Agaji ta Red Cross ta ce yanzu haka akwai mutane sama da dubu 23 da suka ɓata a sassan Najeriya. A bayanin da ta fitar a jiya lahadi, ƙungiyar ta ce 68% na waɗanda suka ɓata dukanninsu mata ne, yayin da jihar Yobe ke matsayin jagora ta fannin yawan waɗanda lamarin ya fi shafa. Fatima Baba Fugu, tana aiki ne da sashen da ke haɗa waɗanda suka ɓata da iyalansu a ƙungiyar ta ICRC daga birnin Maiduguri jihar Borno, ta yi wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal ƙarin bayani a game da waɗannan alkaluma da ƙungiyar ta fitar.
-
Dalilan PDP na baiwa kudancin Najeriya takarar shugaban ƙasa - Sen Ibrahim Tsauri
28/08/2025 Duración: 03minTaron Jam'iyyar PDP a ƙarshen makon da ya gabata, ya amince da bai wa yankin kudancin ƙasar damar gabatar da ɗan takarar zaɓen shugaban ƙaasr da za ayi a shekarar 2027, ya yin da ya haramtawa waɗanda suka fito daga arewacin ƙasar tsayawa takara. Tuni aka bayyana cewar wasu kusoshin jam'iyyar na zawarcin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan da Peter Obi domin tsaya musu takara. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Sakataren jam'iyyar, Sanata Umar Ibrahim Tsauri game da lamarin. Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana.................
-
Janar Idris Bello Danbazau mai ritaya kan taron manyan hafsoshin tsaron Afrika
27/08/2025 Duración: 03minManyan hafsoshin tsaron ƙasashen Afrika sun bayyana aniyar aiki tare a tsakaninsu domin tunƙarar matsalolin tsaron da suka addabi nahiyar, musamman ayyukan ta'addanci. Wannan ya biyo bayan taron da suka halarta a Najeriya. Dangane da wannan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Janar Idris Bello Danbazau mai ritaya dangane don jin alfanun wannan sabin yunƙuri , ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana akai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
-
Malam Isa Sunusi kan kisan da Isra'ila ta yi wa ƴan jaridu a Gaza
26/08/2025 Duración: 03minƘungiyar Amnesty International ta yi Allah wadai da kisan ƙarin ƴan jaridu 5 da Isra'ila ta yi a asibitin Khan Younes. Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Malam Isa Sanusi ya buƙaci ƙasashen duniya da su tilastawa Isra’ila mutunta dokokin duniya wajen kare ƴan jaridun da ke gudanar da aikin su a ƙasar. Ku latsa alamar sauti don jin yadda tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris ta gudana............
-
Baba Ngelzerma kan rashin goyon bayan ta'addancin wasu ɗai-ɗaikun Fulani ke yi
25/08/2025 Duración: 03minƘungiyar Fulani ta Miyetti Allah a Najeriya, ta nesanta kan ta daga goyan bayan ayyukan ta'addancin da wasu ɗai-ɗaikun ƴaƴanta keyi, tare da bayyana cewar ita ta fi jin raɗaɗin matsalar. Shugaban ƙungiyar Baba Usman Ngelzerma ya ce aƙalla Fulani 20,000 aka kashe, yayin da suka yi asarar shanu sama da miliyan 4 ga ayyukan ta'addancin a shekaru 5 da suka gabata. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris.............
-
Kafafen sadarwa sun zama babbar barazana ga zaman lafiyar Najeriya- Majalisa
22/08/2025 Duración: 03minMajalisar Dattawan Najeriya ta bayyana cewar ya zama dole ta yi dokokin da za su takaita yadda kafofin sada zumunta ke neman haifar da tashin hankali a cikin kasar. Shugaban masu rinjaye a Majalisar Bamidele Opeyemi ya bayyana haka, sakamakon zargin neman jefa kasar cikin tashin hankalin da matasa ke yi ta wadannan kafofi. Dangane da wannan yunkuri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar sadarwa,Malam Umar Saleh Gwani. Latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana...
-
Dr Abubakar Sadiq Muhammad kan matsalolin tsaro a Najeriya
21/08/2025 Duración: 03minGwamnan Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya, Uba Sani ya ce matakin soji kawai ba zai iya magance ayyukan ta'addancin da ake fuskanta a ƙasar ba. Gwamnan ya ce ya zama wajibi a magance matsalolin da ke haifar da matsalar baki ɗaya da suka haɗa da talauci da nuna banbanci da rashin shugabanci na gari da kuma bai wa matasa dama. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abubakar Sadiq Muhammad, tsohon malami a jami'ar Ahmadu Bello akan matsalar ta tsaro a ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu...................
-
Farfesa Balarabe Sani Garko kan rage farashin wanke ƙoda a wasu asibitocin Najeriya
20/08/2025 Duración: 03minShugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a faɗin ƙasar. Daniel Bwala, mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan Bayanan da suka shafi tsare-tsaren gwamnati ne ya bayyana hakan a shafin sada zumuntansa na X, inda ya ce matakin zai sauƙaƙa wa dubban marasa lafiya masu fama da ciwon ƙoda. An fara aiwatar da wannan mataki a manyan asibitoci kamar FMC Ebute-Metta da ke Lagos da FMC da ke Jabi a Abuja da UCH Ibadan da FMC Owerri da UMTH Maiduguri, yayin da za a ƙara wasu kafin ƙarshen shekara domin samun damar amfani da su a duk faɗin ƙasar. Sai dai da safiyar Laraba bayan rahotannin RFI, Gwamnatin Najeriya ta ɗan daidaita jerin sunayen manyan asibitocin ƙasar da za su ci gajiyar sabon tallafin domin sauƙaƙawa majinyta wanke ƙoda, inda aka ƙara asibitin koyerwa na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano. Cikin sanarwar da ma'aikatar lafiyar ƙasar ta fitar, ta ce za'a ci gaba da ƙara wasu asibitocin ne dama sannu a hankali, amma
-
Farfesa Yusuf Abdu Misau akan rungumar abinicin da aka sauya wa halitta
19/08/2025 Duración: 03minGwamnatin Najeriya ta bayyana shirin amfani da malaman addini wajen wayar da kan jama'a wajen rungumar amfani da abincin da aka sauyawa kwayar halitta da ake kira GMO. Shugaban hukumar kula da irin wadannan abinci Farfesa AbdullahI Mustapha ya bayyana haka a tattaunawarsa da RFI Hausa. Ganin yadda jama'a ke dari darin amfani da irin wannan abinci, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin kula da harkar lafiya, Farfesa Yusuf Abdu Misau, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Tattaunawa da Janar Kukasheka mai ritaya kan kama shugabannin ƙungiyar Ansaru
18/08/2025 Duración: 03minGwamnatin Najeriya ta bayyana nasarar kama shugabannin ƙungiyar ƴan ta'adda da ake kira Ansaru mai alaƙa da Al'Qaeda, wadda tayi ƙaurin suna wajen kai munanan hare hare a jihohin Neja da kwara. Mai baiwa shugaban ƙasar Najeriya a kan harakokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bada wannan sanarwar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Tsofan kakakin runduna sojin Najeriya Janar Sani Usman Kukasheka ga kuma yadda zantawarsu ta gudana. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hira......
-
Alhaji Mustapha Yusuf Mai Kalwa kan faɗuwar farashin kayan abinci a Najeriya
15/08/2025 Duración: 03minRahotanni daga sassan Najeriya na bayyana faɗuwar farashin kayan abinci, abinda zai taimakawa talakawa wajen samun sauki. Sai dai manoman ƙasar na ƙorafi a kan asarar da suka ce sun tafka. Domin tabbatar da samun saukin farashin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƴan kasuwar hatsi ta duniya da ke Dawanau a jihar Kano, Alhaji Mustapha Yusuf Mai Kalwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattawaunawar tasu.............
-
Abdulhakeem Funtuwa kan yunkurin dakatar da yaƙin Ukraine wajen mantawa da Gaza
14/08/2025 Duración: 03minA ranar Jumma'a ake saran shugaban Amurka Donald Trump zai yi wata ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin dangane da yadda za'a kawo ƙarshen yaƙin da ake gwabzawa a Ukraine. Sai dai wasu da bayyana damuwa kan yadda shugabannin suka manta da batun tsagaita wuta a yaƙin Gaza, ganin yadda ake ci gaba da asarar rayukan ɗimɓin rayuka. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. Abdulhakeem Garba Funtuwa dangane da yunkurin ƙasashe duniyar na samaun tsagaita wuta da kuma watsi da halin da ake ciki a Gaza.