Bakonmu A Yau

Dakta AbdulHakim Garba Funtua akan harajin da Trump ya lafta wa duniya

Informações:

Sinopsis

Ƙasashe da dama ciki har da na Ƙungiyar EU, sun alwashin mayar da martanin ƙaƙaba wa kayayyakin Amurka haraji, kamar yadda shugaba Trump ya ƙaddamar da sabon tsarin karɓar harajin da ya ce ya shafi duniya baki ɗaya.Sabon harajin dai ya kama ne daga kashi 10 zuwa sama, wanda ya shafi hajoji daga kowace ƙasa, matakin da Trump matakin ya ce ya ɗauka ne don kare buƙatun al’ummar Amurka. Don jin yadda masana ke kallon sabon yaƙin kasuwancin, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta AbdulHakim Garba Funtua.