Bakonmu A Yau

Injiniya Safiya Sanusi: Kan sallamar Mele Kyari daga shugabancin NNPC a Najeriya

Informações:

Sinopsis

Kamar yadda wataƙila aka ji cikin labarun duniyar da suka gabata, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayi tankaɗe da rairaya a fannin man fetur ɗin ƙasar inda ya sallami shugaban kamfanin NNPCL malam Mele Kyari da shugaba da mambobin majalisar aminattu na kamfanin. Nan take ne kuma shugaba Tinubun ya maye gurbin manyan jami’an da ya sallama. Ko yaya ƙwararru ke kallon wannan sauyi? Wakilinmu a Abuja Muhd Sani Abubakar ya tattauna da Injiniya Safiyya Sanusi, ƙwararriya a fannin man fetur da Iskar Gas.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar