Bakonmu A Yau
Farfesa Sadiq: Sabon nau'in cutar Polio ya karaɗe wasu jihohin Najeriya
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:03:32
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce an samu ɓullar sabon nau’in cutar Polio a ƙananan hukumomi 18 da ke wasu jihohin Najeriya 9 ciki har da Kano. Rahoton ya ce zuwa yanzu an samu rahotanni daban daban aƙalla 18 kan ɓullar sabon nau’in cutar ta Shan Inna, kuma an tattara bayanan ne a cikin watanni uku da suka gabata zuwa yanzu.Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Sadiq Isa Abubakar, shugaban cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa na asibitin Malam Aminu Kano da kuma jami'ar Bayero.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu