Bakonmu A Yau

Dalilin da ya sa ƴan adawar Najeriya ke sauya sheƙa zuwa APC

Informações:

Sinopsis

‘Yan adawa a Najeriya sun zargi gwamnatin ƙasar ta jam’iyyar APC da yi musu rinto ta hanyar amfani da ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa da ke hannunta da kuma wasu dabaru wajen sanya jiga-jigai daga ɓangaren su ‘yan adawar sauya sheka zuwa ga jam’iyya mai mulki.  Wannan lamari ya maido da muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya a kan dalilan da suke haddasa yawaitar sauyin shekar ‘yan siyasa daga ɓangaren adawa zuwa gwamnati.Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Kamilu Sani Fagge na jami’ar Bayero a Najeriya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyarsu