Bakonmu A Yau

Maitre Lirwanou Abdourahman kan ficewar Nijar Mali da Burkina Faso daga ICC

Informações:

Sinopsis

Burkina Faso, Mali da kuma Nijar sun sanar da janyewar ƙasashensu daga Kotun Hukunta Laifufuka ta Duniya da ke birnin Hague. A sanarwar haɗin-gwiwa da suka fitar cikin daren litinin da ta gabata, ƙasashen uku sun ce sun ɗauki matakin saboda sun lura cewa kotun ta rikiɗe domin zama ƴar amashin ƴan mulkin mallaka. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani dokokin ƙasa da ƙasa Maitre Lirwanou Abdourahman, domin jin ko wataƙila ya yarda da dalilan da wadannan ƙasashe suka gabatar. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.