Bakonmu A Yau

Farfesa Tukur Abdulƙadir kan ƙarin ƙasashen da ke amincewa da Falasɗinu

Informações:

Sinopsis

Ƙasashen duniya na ci gaba da nuna amincewarsu da samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu, a wata guguwa wadda ba’a taɓa ganin irinta ba. Ƙasashen turai da ake ganin suna da ƙyakyawar alaƙa da Amurka irinsu su Burtaniya, Canada da kuma Australia a wannan Karo sun sanar da amincewar su da baiwa Falasɗinu damar zama ƙasa mai cin gashin kanta amma bisa wasu shariɗoɗi. A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce har yanzu da sauran rina a kaba don kuwa amincewar waɗannan ƙasashe ƙadai a fatar baki bata wadatar ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.