Bakonmu A Yau
Tattaunawa da tsohon Jakadan Kamaru Ambasada Malam Mohamed Sani kan zaɓen ƙasar
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:03:38
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
A ƙarshen wannan mako ne za a ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru, zaɓen da zai gudana a ranar 12 ga watan gobe na Oktoba. To sai dai yayin da jam’iyyar RDPC mai mulki ta bayyana Paul Biya a matsayin wanda zai tsaya mata takara, a nasu ɓangare kuwa, yanzu haka ƴan adawa, na ci gaba da tattaunawa don fitar da mutum ɗaya da zai tsaya zaɓen amadadinsu. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ambasada Malam Mohamed Sani, tsohon jakada a lokacin mulkin Ahmadou Ahidjo, amma a yanzu yake zaune a ƙetare, inda ya bayyana yadda suke kallon wannan zaɓe.