Bakonmu A Yau

Ambasada Mohamed Sani kan zaɓen shugaban ƙasa da za a yi a Kamaru

Informações:

Sinopsis

A ƙarshen wannan mako ne za a ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar 12 ga watan gobe na Oktoba idan Allah ya kai mu a Kamaru. To sai dai yayin da jam’iyyar RDPC mai mulki ta bayyana Paul Biya a matsayin wanda zai tsaya mata takara, a nasu ɓangare kuwa, yanzu haka ƴan adawa, na ci gaba da tattaunawa don fitar da mutum ɗaya da zai tsaya musu takara a zaɓen. Kan haka Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ambasada Malam Mohamed Sani, tsohon jakada a lokacin mulkin Ahmadou Ahidjo, amma a yanzu yake zaune a ƙetare, inda ya bayyana yadda suke kallon wannan zaɓe. Ƙu latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............