Bakonmu A Yau

Shugabannin ƙananan hukumomin Kwara sun sanar da rufe kasuwannin sayar da shanu

Informações:

Sinopsis

Shugabannin ƙananan hukumomi a yankin Kudancin jihar Kwara ta Najeriya sun sanar da rufe dukkannin kasuwannin sayar da shanu da aka fi sani da {Kara}. Mahukuntan sun ce sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon tashin matsalolin tsaro da ake samu a kasuwannin. A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara shugaban ƙungiyar Miyetti Allah reshen jihar ta kwara, kuma guda daga cikin jagororin ƙungiyar kasuwannin kara na jihar Alhaji Shehu Garba ya ce sam basu yarda da wannan mataki ba. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar tasu....