Bakonmu A Yau

Tattaunawa da Dakta Bolori akan rage kudin ruwa da babban bankin Najeriya ya yi

Informações:

Sinopsis

Babban bankin Najeriya CBN ya sanar da rage kuɗin ruwan da ake sanyawa masu karɓar bashi daga kaso 27.50 zuwa kaso 27 karon farko cikin shekaru huɗu. Wannan ci gaba na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar tattara haraji ta Najeriya ke cewa ta sami ƙarin kuɗaɗen shiga da kaso 411%, amma hakan ba zai hana ci gaba da ciyo bashi da Najeriya ke yi ba.   A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara, Dr Ahmad Bolori masanin tattalin arziki a Najeriya ce, ragin kwabo 50 kachal yayi matuƙar kaɗan duk da cewa babu wani abu da talaka zai mora a wannan ci gaba. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance.