Informações:
Sinopsis
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
Episodios
-
Bayani a kan kamanceceniyar mulkin gurguzu da kama-karya
04/05/2024 Duración: 20minShirin, wanda ke zuwa muku duk mako a lokacin irin wannan, yana kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wasu daga cikin masu bibiyanmu suka aiko mana ne, kuma a yau, za ku ji amsar tambayar da ke neman ƙarin bayani a kan salon mulkin gurguzu, da kuma ko da gaske yana da kamanceceniya da mulkin kama-karya kamar yadda masu kushe shi ke fadi. Sai a kasance tare da mu.
-
Hukumar samar da wutar lantarki ta yi bayani game da kudin wuta da jama'a za su biya a Najeriya
13/04/2024 Duración: 20min‘Tambaya Da Amsa’ shiri ne da ke kawo amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Bayan janye tallafin lantarki a Najeriya, hukumar samar da wutar ta yi bayani game da rukunnai dabam dabam na masu amfani da wuta da abin da za su biya a matsayin kudin wuta. A yi mun ƙarin bayani a kan wadannan rukunnai. Menene ya sa dole sai an kasa al’umma zuwa rukuni -rukuni?
-
Ƙarin bayani kan yakin duniya da yadda za'a kauce wa sake barkewarsa
30/03/2024 Duración: 20minShirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a kan yakin duniya da yadda za a kauce wa aukuwar wani yakin duniya.
-
Sanadin katsewar kafofin sadarwa na Internet a nahiyar Afirka
23/03/2024 Duración: 20minshirin a wannnan mako zai ba da hankali ne akan abinda ya kai ga katsewar hanyoyin sadarwa na internet a wasu sassa na Nahiyar Afirka.
-
Karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol
16/03/2024 Duración: 20minShirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa mukua wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, za mu ji karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol. Abokinku, Michael Kuduson ne ke muku lale marhabun.
-
Neman bayanni a game da mayar da kasa saniyar ware
09/03/2024 Duración: 20minKamar yadda muka saba, shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayanni a game da mayar da kasa saniyar ware, da kuma tasirin haka a kan kasar da aka maida saniyar ware.
-
Amsoshin wasu daga cikin tambayoyin masu saurare daga Rfi
02/03/2024 Duración: 20minA cikin shirin na wannan mako,Michael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyin,ko wadanan hanyoyi ne ake bi domin samun tikiti kujerar wakili a Kwamity tsaro na MDD.Ya kuma duba wasu tambayoyi da suka jibanci bangaren tsaro da sauren su.
-
Tarihin yan tawayen Houthi na Yemen
17/02/2024 Duración: 20minA cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako, Michael Kuduson ya mayar da hankali a tambayar da ta shafi yan Tawayen Houthi na kasar Yemen.Sai ku biyo mu.
-
Tambaya da Amsa: Cikakken tarihin Hausawa 'yan asalin kasar Mali
10/02/2024 Duración: 20minDaga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin tarihin Hausawa ‘yan asalin kasar Mali. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.
-
Ko me ya sa gwamnonin jihohi a Najeriya ba su da iko a kan jami’an tsaro?
03/02/2024 Duración: 20minShirin ‘Tambaya Da Amsa’ yana kawo muku amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana ne, kuma duk mako yake zuwa muku a daidai wanna lokaci, kuma a wannan tasha. Ko me ya sa gwamnonin jihohi a Najeriya ba su da iko a kan jami’an tsaro? Wannan tambayar na daya daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau. Sai ku kasance tare da abokinku, Michael Kuduson.
-
Neman karin bayani a kan Somaliland da ko kasa ce mai ‘yanci?
27/01/2024 Duración: 20minShirin ‘Tambaya Da Amsa’ yana zuwa muku ne da amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wsu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako ya ke zuwa muku a daidai wannan lokaci.Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman karin bayani a kan Somaliland da ko kasa ce mai ‘yanci. Sai a biyo
-
Bayani a kan ramukan sararin samaniya (Black Holes)
20/01/2024 Duración: 19minKamar yadda aka saba, shirin yana kawo muku amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana ne, kuma duk mako yake zuwa muu a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa, akwai wadda ke neman bayani a kan ramukan nan da ke sarari, wadanda ake kira ‘black holes.
-
Dalilan da suka hana kasashe masu tasowa dogaro da kansu a bangaren tsaro
16/12/2023 Duración: 19minShirin ‘Tambaya Da Amsa ‘ yana zuwa muku ne kowane mako a wannan tasha, inda ya ke kawo amsoshin tambayoyin da suka samu shiga daga masu sauraronmu. Daga cikin tambayoyi da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayani a kan dalilin da ya sa kasashe masu tasowa ba iya dogaro da kan su wajen yaki da matsalar tsaro,, musamman ma ta’addanci da sauransu.
-
Bayani a kan masu 'kujerar naki' a Majallisar Dinkin Duniya
18/11/2023 Duración: 20minShirin 'Tambaya Da Amsa' na wannan mako kaamar kowane mako, ya kawo muku tambayoyi ne da masu sauronmu suka aiko mana, inda ya samar da amsoshinsu daidai gwargwadon iko. Daga cikin tambayoyin da muka amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin yadda aka yi wasu kebabbun kasashe suka samu "kujerar naki' a Kwamitin Tsaro nna Majalisar Dinkin Duniya.
-
Tambaya dangane da bayani a kan kisan kare dangin Holocaust
11/11/2023 Duración: 20minTambaya daga Alhaji Haruna Kira da Umar Ladan Baturiya daga jihar Jigawa Najeriya. So suke a banbanta musu tsakanin ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga. Ko akwai dokar da ke hana amfani da karfi fiye da kima a kan irin wadannan masu aikata manyan laifuka?
-
Amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraron RFI
04/11/2023 Duración: 20minMe ake nufi da karbar rance na biliyoyin daloli don tallafa wa naira kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yanzu ta yi. Mataki ne mai fa’ida? Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ ne ke zuwa ma mai sauraro daga sashen Hausa na Radio France Internationale RFI. Ana iya aiko da tambayar da ake da ita ta adireshinmu na imel a rfihausatambayoyi@gmail.com .
-
Bayani a kan ramin mafi tsawo a duniya, wadda ke gabashin nahiyar Afrika
28/10/2023 Duración: 20min‘Tambaya Da Amsa’, daga sashen Hausa na Radio France Internationale, RFI, tare da abokin nan naku, Michael Kuduson.Shiri ne da ke kawo muku amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana, duk mako yake zuwa daga wannan tasha, kuma a lokaci irin wannan. Daga cikin tambayoyn da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayani a kan ramin nan mafi tsawo a duniya, wadda ke gabashin nahiyar Afrika, wato East African Rift.
-
Karin bayani a kan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya
21/10/2023 Duración: 20minShirin yana zuwa muku ne da wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha, kuma a daidai wannan lokaci. A cikin Shirin wannan makon, zai amsar tambayar da ke neman Karin bayani a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma gazawarsa da ma majalisar wajen kawar da yake yake a duniya,
-
Dalilan da suka haddasa barkewar yaki tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas
14/10/2023 Duración: 20minShirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Micael Kuduson, mayar da hankali kan neman karin bayani dangane da musabbabin sake barkewar rikici tsakanin kungiyar Hamas ta yankin Falasdinu da Isra’ila. Akwai kuma wasu karin tambayoyin da shirin ya yi wa masu sauraro karin bayani akai.
-
Shirin Tambaya da Amsa na wannan mako ya tabo batun cutar dake maida mutum zabaya
30/09/2023 Duración: 20minkamar yadda aka saba a ko wane mako shirin Tambaya da Amsa tare da Michael KJuduson, na mayar da hankali wajen amsa muhimman tambayoyin da kuka buka ci fita daga jahilcinsu. ina a wannan mako, shirin ya tabo batutuwa da dama, da suka hada da son sanin irin cutar dake kone fatar bakaken fata ta na zama farar sal.