Sinopsis
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.
Episodios
-
Yadda ɗalibai a Bauchi ke watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai
01/04/2025 Duración: 10minShirin wannan makon zai yi dubi ne akan yadda ɗalibai a jihar Bauchi ke yin watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai.Jihar Bauchi, ta yi ƙaurin suna a baya a matsayin wadda ke sahun gaba wajen yawan yaran da suka yi watsi da makarantunsu tare da rungumar harkar tonon ma’adinai don samun dogaro da kai.Dalili ke nan da fiye da rabin daliban wasu makarantun firamare a jihar, suka bar zuwa makaranta inda suka karkatar da hankali kan harka haƙon ma’adanan.
-
Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin ɗaukar nauyin karatun ƴaƴa mata zuwa PHD
25/03/2025 Duración: 09minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya maida hankali ne kan shirin da gwamnatin jihar Jigawa ta ƙaddamar, na ɗaukar nauyin karatun ‘ya’ya mata daga Firamaren har zuwa karatun Digirin Digirgir, shirin da ta ce tana fatan zai zaburar da ƙarin mata da iyayensu wajen duƙufa neman ilimi, ba tare da fargabar fuskantar ƙalubale na rashin ƙarfi ta fuskar tattalin arziƙi ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman.........
-
Gwamnatin Ghana na nazarin yiwuwar fara bayar da ilimin Sakandire kyauta
04/03/2025 Duración: 09minShirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan shirin gwamnatin Ghana na fara bayar da ilimin Sakandire kyauta, kodayake an faro da sauraren ra'ayin jama'a kan wannan shiri wanda ma'aikatar ilimin ƙasar ta bijiro da shi. Bayanai sun ce baya ga bayar da ilimin kyauta, tsarin zai kuma kawo gyara a yanayin bayar da ilimi musamman a manyan makarantun ƙasar ta Ghana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
-
Yadda matasa a Najeriya suka ƙirƙiri injin da ke tsince tsakuwa daga Shinkafa
25/02/2025 Duración: 09minA wannan makon, shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara ya mayar da hankali kan yadda wasu matasa suka ƙirƙiri wani nau'in inji da ke cire tsakuwa daga jikin shinkafa, wanda zai taimaka matuƙa wajen samar da tsaftatacciyar shinkafa. Kafin wannan hoɓɓosa daga matasan, akan shigo da irin injinan ne daga ƙasashe irin China don sauƙaƙawa Manoma.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.