Sinopsis
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episodios
-
Koken 'yan Najeriya na rashin saukar farashin kayan masarufi duk da faduwar Dala
24/04/2024 Duración: 10minShirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan batun korafin ‘yan Najeriya ke yi game da rashin ganin sauyi a farashin kayan amfanin yau da kullum, bayan karyewar farashin ƙudaden ƙetare masamman dalar Amurka da sanadin tashin ta ne ya haddasa mummunan tashin farashin kayayyaki a kasar, wanda har hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce lamaarin ya yi muni. Ko da ya ke a wasu manyan biranen Najeriya irinsu Legas da Abuja, an fara ganin sauƙi a wasu kayayyakin abinci irinsu shinkafa da man girki da dai sauransu.Ku latsala alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba........
-
Yadda matasa suka rungumi kananan sana’o’i lokacin azumin Ramadana a Damagaram
03/04/2024 Duración: 09minShirin Kasuwa a Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan kananan sana’o’i da matasa ke yi don samun na abinci a lokacin azumin watan Ramadana a Damagaram da ke jamhuriyar Nijar. wasu daga cikin sana'oin da matasan sukafi mai da hankali akai dai sun hada da bredi ko kayan marmari ko kayan lambu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......
-
Gidauniyar Dangote ta kashe naira biliyan 15 na tallafin abinci a Najeriya
27/03/2024 Duración: 10minShirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan rabon tallafin abincin naira biliyan 15, da Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar a Najeriya. Wannan dai na daga cikin matakan rage radadin talauci a tsakanin al'ummar Najeriya, da gidauniyyar hamshakin attajirin Afirka ta kaddamar a birnin Kano da ke arewacin kasar. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......