Sinopsis
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episodios
-
Yadda Hausawa ke ƙoƙarin yin watsi da al'adar amfani da kwarya
17/12/2024 Duración: 09minShirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin mancewa da al'adar amfani da kwarya, wacce ke cikin daɗaɗɗun kayan amfanin gida na Malam Bahaushe. To sai dai duk da irin tasirin Kwarya a cikin al’ummar ta Hausawa, sannu a hankalin wannan al’ada tana neman gushewa a tsakanin al’ummar ta Hausawa har ma da Fulani da suka rungumi al’adar daga baya. Masu harkar sayar da ƙore a yankin Arewacin Nigeria, na kokawa sosai kan rashin garawar sana’ar tasu sakamakon yadda Hausawa da Fulani suka rage amfani da Kwarya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
-
UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundinta na al’adun duniya
10/12/2024 Duración: 10minShirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin da Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, na sanya hawan Dabar Kano a arewacin Najeriya cikin kundinta na al’adun duniya.Bincike ya nuna cewar an fara gudanar da al’adar hawa Daba a lokutan bikin ƙaramar Sallah da Babba tun kafin jihadin Shehu Usman Dan fodio zamanin Sarkin Kano Rumfa. Masana a fannin tarihi sun ce zamanin Sarkin Kano Abbas, ya yi wa tsarin sauye-sauye wanda akan sa ake tafiya har zuwa wannan lokaci.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
-
Gushewar al'adar tatsuniya a cikin al'ummar Hausawa
26/11/2024 Duración: 10minShirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya tattauna dangene da gushewar a'adar tatsuniya wadda ke zama hanyar da al’ummar Hausawa ke amfani da ita wajen ilmantarwa, fadakarwa da kuma tarbiyantar da yara ta hanyar shirya kagaggun labarai masu kunshe da darussa.
-
Tattaunawa da Mai Martaba Sarkin Nassarawa a Najeriya
21/11/2024 Duración: 09minA yau shirin al’adun zai je jihar Nassarawa inda muka samu zantawa da mai Martaba Sarkin Nassarawa,daga bisani za mu je Jamhuriyar Nijar inda zamu duba koma bayan wakokin gargajiya a cikin al’umma.