Sinopsis
Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.
Episodios
-
Taba Ka Lashe: Al'adar bikin aure a Guddiri
15/03/2022 Duración: 09minAure na daya daga cikin al'adun da Guddurawa suke masa hidima ta gani a fada fiye da duk wata al'adar su, kama daga farkon nema tsakanin saurayi da budurwa har zuwa lokacin bayarwa da mai gaba daya lokacin bikin auren. Kuma har zuwa yanzu guddurawa ba su bari ba. Wannan shi ne batun a shrin Taba Ka ashe na wannan mako ya yi duba a kai. Daga kasa za a iya sauraon sauti
-
Taba Ka Lashe: Al'adar bikin aure a Guddiri
15/03/2022 Duración: 09minAl'adar bikin aure a Guddiri a Jihar Bauchi dadaddiyar masarauta ce mai dumbin tarihi, kuma guddurawa suna da wasu fitattun al'adunsu da suka banbanta su da sauran masarautun Bauchi.
-
Taba Ka Lashe: 02.03.2022
08/03/2022 Duración: 09minKo har yanzu ana amfani da wakokin gargajiya da kayan kidan harshen Hausa a kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: Rayuwar Musulmi da Kirista
15/02/2022 Duración: 09minMusulmi da Kirista a Jihar Filaton Najeriya na zaune a unguwani dabam-dabam sabanin yadda a baya al'ummomin biyu ke zaune wuri guda suna cudanya.
-
Taba Ka Lashe 02.01.2022
08/02/2022 Duración: 09minShirin na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan kirari. Ya al'adar kirari take a kasashen Afirka?
-
Taba Ka Lashe: 26.01.2022
01/02/2022 Duración: 09minShirin na wannan lokaci ya ziyarci jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, inda ya gano wani Masallaci da ya kwashe shekaru aru-aru.
-
Taba Ka Lashe: 29.12.2021
04/01/2022 Duración: 09minKo kun san su wanene mafarauta da 'yan tauri da kuma yadda suke samun taurin? Ku saurari Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 22.12.2021
28/12/2021 Duración: 10minShirin ya duba yunkurin farfardo da wata sarautar gargajiya ta kabilar Abzinawa a garin Afess na jahar Agadez a Nijar.
-
Taba Ka Lashe: 15.12.2021
21/12/2021 Duración: 09minAn gudanar da bikin nadin sababbin sarautu, a masarautar Hausawan Turai. Karin bayani cikin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 08.11.2021
14/12/2021 Duración: 09minMata na taka muhimmiyar rawa, wajen magance rikice-rikicen kabilanci da na addinai da makamantansu. Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 24.11.2021
30/11/2021 Duración: 09minKo kun san yadda mabiya darikun Sufaye ke ziyara Kushewar Waliyai a Maroko? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe
16/11/2021 Duración: 09minWurin da ake tsugune da daruruwan mata da ake zargi da aikata maita a wata cibiya ta musamman da ake wa lakabi da "Sansanin mayu” a arewacin Ghana.
-
Taba Ka Lashe: 27.10.2021
02/11/2021 Duración: 09minA duk ranakun 12 ga watan Rabi'ul Auwal na ko wacce shekara, al'ummar Musulmi a fadin duniya kan yi bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAAW). A wannan shirin mun yi nazarin yadda aka gudanar da bukukuwan na bana a jihar Kano da ke Najeriya.
-
Taba Ka Lashe 22.09.2021
28/09/2021 Duración: 09minYadda zamani ke shirin gusar da al'adun gargajiyan jahar Gaya a jamhuriyar Nijar. Latsa kasa don jin cikakken shirin.
-
Taba Ka Lashe: 15.09.2021
21/09/2021 Duración: 10minAmfani da ahnnun hagu, halitta ce da daga Allah. Sai dai wasu na fuskantar kalubale sakamkon wasu al'adu da ma addinai. Ku saurari shirinmu na Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 01.09.2021
07/09/2021 Duración: 09minKo kun san yadda kabilar Igbo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, ke bikin binne gawa? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba ka lashe 04.05.21
31/08/2021 Duración: 09minAl'adar wasan kara a yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar wanda matasa ke yi a lokacin kaka bayan girbin amfani gona
-
Taba Ka Lashe: 11.08.21
24/08/2021 Duración: 10minKo kun san cewa akwai fadar Hauasawa har ma da sarkinsu a Turai? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan batun wannan sarauta.
-
Taba Ka Lashe: 04.08.2021
10/08/2021 Duración: 09minKo kuna da masaniya kan yadda al'adar wasan kara ke gudana a jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar? Shirin Taba Ka Lashe
-
Taba Ka Lashe: 21.07.2021
27/07/2021 Duración: 09minShadi, dadaddiyar al'ada ce ta Fulani da aka fi amfani da ita wajen neman aure. Sai dai a yanzu al'amura sun sauya. Ko ya al'adar ta shadi take gudana a yanzu? Shirin Taba Ka Lashe.