Sinopsis
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episodios
-
Yadda ake samun ƙaruwar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a
25/11/2024 Duración: 10minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya nazarci yawaitar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a da ake ganin ta’azzararsu a wannan lokaci musamman a sassan Najeriya a wani yanayi da matsi ko kuma tsadar rayuwa ke ci gaba da galabaitar da jama’a. Dai dai lokacin da masana ke alaƙanta wannan matsala ta mutuwar far ɗaya da wasu kwantattun cutuka da yanayi kan tayar da su a lokaci guda, wani bincike baya-bayan nan ya danganta tsananin damuwa da yawaitar tunane-tunne halin rayuwa a matsayin ummul aba’isin kamuwa da wasu cutuka da ke kisan jama’a. Tuni dai masana a ɓangaren kiwon lafiya suka tsananta kiraye-kirayen ganin jama’a sun mayar da hankalin wajen sanin halin da lafiyarsu ke ciki don kaucewa mutuwar ta kwaf ɗaya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......
-
Lafiya Jari ce: Illar da hayaƙin girki ke yiwa lafiyar idon Mata
11/11/2024 Duración: 10minA wannan makon shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani gargaɗin masana game da illar hayaƙi ga lafiyar jama’a a wani yanayi da masanan ke ganin mazauna garuruwa irin Kano da Sokoto da Kwara baya ga kaso mai yawa na jihohin arewacin Najeriya na cikin haɗarin kamuwa da cutukan masu alaƙa da numfashi sakamakon yadda suka dogara da itace ko kuma gawayi wajen yin girki. A ɓangare guda wasu ƙwararrun na ganin matan da suka shafe lokaci suna girki da itace ka iya fuskantar matsalar ido, tambayar a nan ita ce ko matan na da masaniya kan illar hayakin girki ga lafiyar idonsu? Ku biyo mu a cikin shirin don sauraren mahangar masana da kuma yadda Mata ke kallon illar ta hayaƙin girki ga lafiyarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
-
Yadda cutar kwalara ta addabi wasu jihohin arewacin Najeriya
04/11/2024 Duración: 09minShirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar Kwalara ko Amai da Gudawa da ta afkawa wasu jihohin Najeriya, inda ta haifar da asarar ɗumbin rayuwa tun bayan ɓullarta a farkon wannan shekara ta 2024
-
Ƙuncin rayuwa na jefa ɗimbin ƴan Najeriya cikin tsananin damuwa - Rahoto
28/10/2024 Duración: 09minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan matsalar damuwa mai dankwafarwa ko tsananin damuwa da ake kira Depression, cutar da ake ganin ta’azzararta a baya-bayan nan tsakanin ƙasashe masu tasowa musamman waɗanda ke fama da matsi ko kuma ƙuncin rayuwa. Wasu bayanan ƙwararru yayin bikin ranar lafiyar ƙwaƙwalwa da ya gudana a farkon watan nan, ya nuna yadda matsi da ƙunchin rayuwa ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya a tsananin damuwar ko kuma damuwa mai dankwafarwa, matsalar da likitoci suka yi gargaɗin cewa ka iya kaiwa ga taɓin ƙwaƙwalwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........