Sinopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodios
-
Ra'ayoyin masu saurare kan yajin aikin lauyoyi a Nijar
14/08/2025 Duración: 09minLauyoyi a Jamhuriyar Nijar sun tsunduma yajin aikin kwanaki biyu daga yau Alhamis, domin nuna rashin amincewa da rusa ƙungiyoyin alƙalai da sauran ma’aikatan shari’a da gwamnatin ƙasar ta yi. Kafin rusa waɗannan ƙungiyoyi, tuni aka rusa ƙungiyoyin jami’an kare gandun daji da na kwastam da kuma illahirin jam’iyyun siyasar ƙasar. Shin, ko me za ku ce a game da wannan mataki na gwamnatin Nijar ta ɗauka? A irin wannan yanayi, ko meye makomar ƴancin gudanar da ƙungiyoyi a ƙasar? Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi...
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda Bankin Duniya ya rantawa Najeriya dala miliyan 300
13/08/2025 Duración: 10minBankin Duniya ya amince ya ranta wa Najeriya dala miliyan 300 kwatankwacin naira biliyan 460 don tallafa wa mutanen da suka ƙaurace wa matsugunansu saboda matsaloli a sassa daban daban na Arewacin ƙasar. Yanzu haka akwai mutane sama da milyan 3 da rabi da ke rayuwa a wannan yanayi, kuma mafi yawansu sun dogara da tallafi ne domin rayuwa. Shin ko waɗanne matakai suka kamata a ɗauka don tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen ta hanyoyin da suka dace? Sai ku bayyana ra’ayoyinku a lambarmu ta Whatsapp da kuma shafinmu na Facebook.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan yadda ake samun ambaliyar ruwa a irin wannan lokaci
12/08/2025 Duración: 10minKusan a kowacce shekara, dai-dai wannan lokaci ne ake samun faruwar ambaliya sakamakon saukar ruwan sama mai yawa da ke haddasa asarar rayuka da kuma dukiyoyi masu tarin yawa. A daidai wannan lokaci, ko wane hali ake ciki a yankunanku dangane da batun ambaliya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a wannan rana. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan matakin Nijar na ƙwace kamfanonin haƙar zinare
11/08/2025 Duración: 10minGwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace ilahirin kamfanonin haƙo zinare tare da shelanta cewa sun zama mallakin ƙasar, yayin da a ɗaya ɓangare ta hana fitar da duk wani nau’in dutse mai ƙima zuwa ƙetare sai tare da izinin hukuma. Hakan na zuwa ne watanni bayan ta ƙwace kamfanonin haƙo uranium matsayin mallakin ƙasar. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...