Sinopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodios
-
Ra'ayoyin masu saurare game da yaƙin neman zaɓen Kamaru
29/09/2025 Duración: 10minAn ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasar Kamaru, inda mutane 12 ciki har da shugaba mai-ci Paul Biya za su kara da juna a ranar 12 ga watan gobe na Oktoba idan Allah ya kai mu. Yayin da Paul Biya ke fatan sake samun yardar al’umma don ci gaba da mulki karo 8, a nasu ɓangare kuwa 'yan adawa na kallon zaɓen a matsayin wata dama don samar da sauyi a ƙasar. Shin me za ku ce a game da wannan yaƙin neman zabe? Ko wane fata ku ke yi wa al’ummar Kamaru? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
-
Ra'ayoyi kan shirin Amurka na hana ƴan Najeriya masu rashawa shiga ƙasar
25/09/2025 Duración: 09minShirin Ra'ayoyin mai Saurare na wannan ranar Alhamis 25 ga watan Satumbar 2025, wanda Oumar Sani ya gabatar, ya tattauna ne kan matakin gwamnatin Amurka na hana duk wani ɗan Najeriya ciki har da jami’an gwamnati da aka samu da hannu da rashawa bisar da za ta ba su damar shiga ƙasar.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ficewar ƙasashen AES daga kotun ICC
24/09/2025 Duración: 10minBurkina Faso, Mali da kuma Nijar sun sanar da janyewa daga Kotun Hukunta Laifuka ta Duniya da ke birnin Hague, bisa zargin kotun da kasancewa ƴar amshin ƴan mulkin mallaka. To sai dai wasu na ganin cewa shugabannin ƙasashen uku sun ɗauki matakin ne don kauce wa bincike ko tuhuma daga wannan kotu. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacinku a yau cikin shirin na Ra'ayoyinku masu saurare. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ɗage haramcin shigar da siminti a Nijar
22/09/2025 Duración: 10minGwamnatin Jamhuriya Nijar ta ɗage haramcin shigar da siminti a ƙasar, sakamakon yadda ake fama da ƙamfarsa, lamarin da ya haifar da tsadarsa a kasuwa. Wani lokaci a can baya ne dai mahukunta suka sanar da haramta shigar da simintin don kare kamfanonin da ke sarrafa shi a cikin gida, amma kuma aka wayi gari na cikin gidan sun gaza wadatar da masu buƙatar sa domin yin gini. Shin ko me za ku ce a game da cire haramcin? Wannan shine maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya
19/09/2025 Duración: 10minYau juma'a, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar faɗin albarkacin bakinsu, kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tattalin arziƙi, ilimi, lafiya, zamantakewa, siyasa da dai sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare Nasiru Sani...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan umarnin gwamnatin Neja na duba khuɗubobi kafin yaɗa su
18/09/2025 Duración: 10minA Najeriya, gwamnatin Neja ta umarci ilahirin limaman masallatan Juma'a a faɗin jihar da su riƙa miƙa mata bayanan da ke ƙunshe a cikin huɗubar da za su gabatar don tantancewa, matakin da Gwamna Muhammadu Umar Bago ke cewa yunƙuri ne na kaucewa duk wata barazana ta cusa ƙiyayya ko kuma haddasa rikici da malaman ka iya yi. Yaya kuke kallo wannan mataki na Gwamnan jihar Neja? Shin kuna ganin akwai buƙatar shigowar gwamnati don daidaita yadda malamai ke gudanar da khuɗubobi da sauran karatuttuka? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
-
Ra'ayoyin masu saurare game da yadda ICPC ke sanya ido kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi
17/09/2025 Duración: 10minHukukumar Yaƙi da Rasha ta ICPC a Najeriya, ta ce yanzu haka tana ƙara sa-ido dangane da yadda ake kashe kuɗaɗe mallakin ƙananan hukumomi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya ke shan matsin lamba domin ganin ta aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli wanda ya buƙaci a zuba wa ƙananan hukumomin kuɗadensu kai-tsaye a maimakon bi ta hannun gwamnonin jihohi. Ko me za ku ce a game da jan ƙafa wajen aiwatar da wannan umarni da kotu ta bayar tun watan Yulin shekara ta 2024 da ta gabata? Wace irin rawa ya dace ICPC ta taka don kare dukiyar ƙananan hukumomi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakin ku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
-
Ra'ayoyin Masu Sauraro kan janye yajin aikin Likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya
15/09/2025 Duración: 09minShirin Ra'ayoyin Mai Sauraro na wannan Litinin tare da Nasiru Sani ya tattauna ne kan janye yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar da ƙugiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta sanar a ƙarshen mako, kwanaki bayan fara ta a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ta ƙara wa'aɗin makwanni biyu don a biya musu buƙatunsu. Daga cikin buƙatun ƙungiyar da take nema gwamnati ta biya akwai abinda ya shafi albashi da alawus-alawus da kuma walwalar mambobinta. Ku latsa alamar sauti domin sauraron ra'ayoyin wasu daga cikin masu sauraro da suka aikoma ta manhajarmu ta Whatsapp
-
Ra'ayoyin masu saurare kan matakin Najeriya na haramta zirga-zirgar jiragen ruwa marasa lasisi
11/09/2025 Duración: 09minA yunƙurin rage yawaitar haɗura akan ruwa, Hukumar Kula da Zirga-zirga a kan Kogunan Najeriya ta haramta yin amfani da jiragen ruwa a kan kogunan ƙasar sai tare da samun izini daga gare ta. Wasu daga cikin matakan da hukumar ta sanar sun haɗa da hana yin lodin fasinja sai a tashoshin da ta amince da su, sai tilasta wa fasinja yin amfani da rigar kariya, da mallakar takardar shaidar ƙwarewa ga illahirin matuƙan jiragen da dai sauransu. Anya waɗannan matakai za su taimaka don rage afkuwar haɗurra a kan kogunan Najeriya? Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ƴancin faɗar albarkacin baki a Nijar
10/09/2025 Duración: 08minA Jamhuriyar Nijar, batun ƴancin faɗin albarkacin baki, aikin jarida ko kafa ƙungiyoyi da sunan yi fafutuka na ci gaba da fuskantar barazana. Bayan rusa ilahirin jam’iyyun siyasa, daga bisani an ci gaba da kama ƴan jarida da masu fafutukar kare hakkin bil adama, tare da jefa ƙungiyoyin kwadago a cikin fargaba ta hanyar farawa da rusa kungiyoyin alƙalai na ƙasar. Ku latsa alamar sauti don jin ra'ayoyin jama'a kan wannan batu.
-
Ra'ayoyin masu sauraren kan rikicin NUPENG da Dangote a Najeriya
08/09/2025 Duración: 10minA Najeriya, an shiga takun-saƙa tsakanin Ƙungiyar NUPENG ta direbobin motocin dakon mai da iskar gas da kuma Ɗangote wanda ya sanar da sayo motoci dubu 4 da zai yi amfani da su don rarraba man fetur a sassan ƙasar. Yayin da NUPENG ke cewa magoya bayanta ne ke da hurumin raba mai da iskar gas a ƙasar, sai dai manazarta na cewa Ɗangote, na da damar raba hajarsa sakamakon sakin mara da aka yi wa ɓangaren kasuwanci a ƙarƙashin dokokin Najeriya. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi....
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa daban-daban
05/09/2025 Duración: 10minKamar yadda aka saba kowacce ranar Juma'a mukan baku dama don bayyana mana ra'ayoyinku game da batutuwa daban-daban da suka shafin fannonin rayuwa daban-daban don kira ga masu ruwa da tsaki da su kawo ɗauki. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Hauwa Aliyu Garba
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kama Simon Ekpa mai fafutukar kafa ƙasar Biafra
03/09/2025 Duración: 10minKotun ƙasar Finland ta ɗaure Simon Ekpa mai fafutukar kafa ballewar Biafra daga Najeriya shekaru 6 a gidan yari, saboda samun sa da laifufukan ta’addanci. Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin ake ci gaba da tsare ɗaruruwan mutane a gidajen yarin Najeriya bisa zargin aikata ta’addanci, amma kotuna sun gaza hukuntar da su. Shin ko me za ku ce a game da wannan hukunci da kotun ƙasar Finland ta yanke? Meye ra’ayoyinku a game da gazawar kotunan Najeriya wajen hukunta waɗanda ake tuhuma da aikata irin waɗannan laifuka a cikin gida? Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu
-
Ra'ayoyin masu saurare kan taron manyan hafsoshin tsaron Afrika
27/08/2025 Duración: 09minHafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka a taron da suka yi a birinin Abujan Najeriya, sun ƙuduri aniyar haɗa gwiwa don tunkarar ƙalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta. Wannan taro dai ya samu halartar wakilan ƙasashe sama da 50, waɗanda suka yi imani da cewa la’akari da girman matsalar, akwai buƙatar ƙasashen su yi aiki a tare don tunkarar ta. Shin ko meye ra’ayoyinku a game da wannan yunƙuri na ƙasashen Afirka? Waɗannan shawarwari za ku bayar domin samun nasarar wannan fata? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
-
Ra'ayoyin masu sauraren kan yadda ɗimbin mutane suka rasa ayyukansu a Nijar
25/08/2025 Duración: 11minA jamhuriyar Nijar, dubban mutane ne suka rasa ayyukansu yayin da ɗimbin ƴan gudun hijira suka daina samun tallafi, bayan da mahukunta suka kori mafi yawan ƙungiyoyin agaji daga gudanar da ayyukansu a cikin ƙasar. Bayan korar waɗannan ƙungiyoyi da ke taimaka wa ƴan gudun hijira, a mafi yawan yankuna har yanzu gwamnatin ta gaza samar da tsarin da zai maye gurbin waɗannan ƙungiyoyi don agaza wa jama’a. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin....
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa da dama
22/08/2025 Duración: 06minYau Juma'a rana ce da mukan baiwa masu saurarenmu damar tofa albarkacin bakinsu a cikin shirinmu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Danna alamar saurare domin jin cikaken shirin tare da Nasiru Sani
-
Ra'ayoyin masu saurare kan alfanun sulhu da 'yanbindiga ko akasanin haka a Najeriya
21/08/2025 Duración: 10minA Najeriya muhawara ta ɓarke game da buƙatar sulhu da ƴan ta’adda maimakon amfani da ƙarfin Soji, kodayake an samu mabanbantan ra’ayoyi daga ɓangaren masana a fannin na tsaro lura da yadda suka ce irin wannan sulhu ya gaza amfanarwa a yankuna da dama duk da cewa anga alfanunsa a wasu yankunan. Yaya kuke kallon wannan batu? Shin kuna ganin sulhu ko kuwa amfani da ƙarfin soji shi ne mafi a’ala wajen yaƙi matsalolin tsaron Najeriyar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkaci bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza....
-
Ra'ayoyin masu saurare kan shirin rungumar GMO a Najeriya
19/08/2025 Duración: 10minLura da yadda jama’a ke ɗari-ɗari a game da kayan abincin da aka sauya wa ƙwayoyin halitta da ake kira GMO, wannan ya sa mahukunta a Najeriya ke neman yin amfani da malaman addini domin gamsar da jama’a su rungumi irin wannan abinci. Abin neman sani a nan shi ne, shin ko kun fahinci abin da ake kira GMO? Ko a shirye ku ke domin karɓar nau’in abincin da aka canza wa ƙwayoyin halitta? Anya yin amfani da malaman addini zai sa jama’a su amince da shi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kama jagororin ƙungiyar Ansaru a Najeriya
18/08/2025 Duración: 10minMai Bai wa Shugaban Najeriya Shawara kan Sha’anin Tsaro Nura Ribaɗo ya tabbatar da kama jagororin ƙungiyar Ansaru da ake kira Ƴan Mahmuda su biyu, waɗanda suka jima suna addabar yankunan ƙasar. Ana dai bayyana wannan ƙungiya a matsayin babbar barazana ga matsalar tsaron ƙasar, saboda alaƙarta kai-tsaye da Alqa’ida. Shin ko wane sauyi wannan kame zai samar ta fannin tsaro a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
15/08/2025 Duración: 09minYau take ranar bayyana ra'ayoyinku kan batutuwa da suke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, zamantewa da sauran abubuwan daban daban na rayuwa. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyin...