Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Tattaunawa da Dr Idris Harbau kan taron ƙasashen BRICS a Brazil
09/07/2025 Duración: 03minA ranar Litinin ƙasashe manbobin ƙungiyar BRICS suka kammala taronsu na 17 a Brazil, inda a cikin kwanaki biyu da suka shafe suna ganawa, jagororin ƙasashen suka tattauna a kan yadda manufofin shugaba Trump ke tasiri kan tattalin arziƙi da kasuwancin Duniya. Sai dai tun kafin kammala taron, shugaba Trump ɗin ya yi barazanar lafta harajin kashi 10 kan kayayyakin ƙasashen na BRICS, da ma duk wata ƙasa da ta goyi bayan matakan adawa da manufofin Amurka. Kan wannan batu, da kuma tasirin ƙungiyar ta BRICS Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau, masanin tattalin arziƙi da ke Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..
-
Tattaunawa da Sakataren ƙungiyar direbobin sufuri ta NURTW kan yawaitar haɗurra
08/07/2025 Duración: 03minRahotanni daga Najeriya sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon haɗurran motoci da aka samu a ƙarshen mako cikin jihohin Kano da Jigawa da Bauchi da Lagos da kuma jihar Oyo baya ga Lagos da kuma jihar Kogi. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin hanyoyin motoci ke ci gaba da taɓarɓarewa, yayinda wasu direbobin ke tuƙi cikin yanayi na maye ko kuma saɓawa dokokin tuƙi. Dangane da wannan matsala da ke kaiwa ga asarar ɗimbin rayuka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Adamu Idris Abdullahi Sakataren ƙungiyar direbobin sufuri ta NURTW da ke Abuja ga kuma yadda tattaunawarsu ta kasance. Sai ku latsa alamar sauti don saurare.
-
Tattaunawa da Honourable Siraj Imam Ibrahim kan ambaliyar ruwan Kano
07/07/2025 Duración: 03minA ƙarshen makon da ya gabata aka samu ambaliyar ruwan sama a sassan birnin Kano, a dai dai lokacin da damina ta fara kankama a jihar. Wannan matsalar ta haifar da matsaloli ga mazauna da kuma baƙin da ke zuwa birnin. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƙaramar hukumar Dala, Hon Siraj Ibrahim Imam, Kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti son sauraron cikakkiyar Hirar.
-
Dr Aliyu Bello kan ƙawancen 'yan adawa a Najeriya
04/07/2025 Duración: 03minA wannan mako ne yan adawan Najeriya suka kafa wani kawancen da suka ce zai tinkari Jam'iyyar APC a zabe mai zuwa, da zummar kawar da ita daga karagar mulki. Shirin Duniyarmu Ayau na RFI Hausa ya gudanar da mahawara tsakanin Sanata Ahmed Babba Kaita na sabuwar kawancen da kuma shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Nasarawa Dr Aliyu Bello. Ga kadan daga cikin abinda shugaban APC ya fadi a cikin shirin da zai zo muku gobe da misalin karfe 5 na yamma.
-
Emmanuel Shehu kan haɗakar jam'iyyun adawa a Najeriya da nufin tunkarar APC mai mulki
03/07/2025 Duración: 03minWasu daga cikin jiga-jigan ƴan adawar Najeriya sun haɗa kansu wajen komawa jam'iyyar ADC domin shirin tunkarar gwamnatin APC mai mulki da suke zargi da rashin iya mulki, Yayin gabatar da sabbin shugabannin, ƴan adawar sun sha alwashin ceto talakan Najeriya daga halin ƙuncin da ya samu kansa. Sai dai wasu na cewa neman mulki ne kawai suke yi amma ba don talakan Najeriya ba. Bashir Ibrahim Idris ya tattauwa da shugaban cibiyar horar da ƴan Jaridu ta IIJ da ke Abuja, Dr Emman Shehu, kuma ga yadda zatawarsu ta gudanar.
-
Dr Yahuza Getso kan yadda jami'an sojoji suka hallaka Kachalla Ɗanbokolo a Zamfara
02/07/2025 Duración: 03minA Najeriya mayaƙan sa kai a jihar Zamfara sun yi nasarar hallaka wasu daga cikin manyan kwamandojin ƴan bindigar da suka hana zaman lafiya a jihar, cikinsu har da Kachalla Ɗanbokolo da wasu tarin magoya bayansu. Domin sanin tasirin wannan nasara ga jama'ar yankin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauba da masanin harkar tsrao, Dr Yahuza Getso. Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar
-
Muhammad Adamu Dansitta kan shirin gwamnatin Najeriya na dasa bishiyoyi biliyan 20
01/07/2025 Duración: 03minGwamnatin Najeriya ta sha alwashin dasa itatuwa biliyan 20, a kokarin da take yi na magance gurgusowar hamada da tsananin zafi , har ma da sauyin yanayi. Mataimakin shugaban kasar Kashin Shetimma ne ya bayyana hakan, yayin da yake jawabi a wajen wani taroa kasar Habasha. Game da tasirin wannan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Muhammad Adamu Dansitta. Dannan alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar.
-
Issof Emoud kan sabuwar Majalisar Tuntuɓa da gwamnatin sojin Nijar da kafa
30/06/2025 Duración: 03minMajalisar Tuntuɓa da gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta kafa ta conseil consultatif na fara aiki a ranar Asabar 28 ga watan Yunin wannan shekara ta 2025, Majalisar mai kunshe da mambobi 194 an ɗaura mata nauyin bayar da shawarwari kan harokin da su ka shafi cigaban ƙasa da kuma gayyato majalisa zartaswa domin amsa tambayoyi idan hakan ta kama. A kan haka Oumar Sani ya tattauna da Hon. Issouf Emoud ɗan majalisa mai wakilta jihar Agadas.
-
Amb Abubakar Chika: cika shekaru 80 da sanya hannu kan yarjejeniyar samar da MDD
26/06/2025 Duración: 03minYau ake cika shekaru 80 da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar da ta samar da Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar a Birnin San Francisco da ke Amurka, a ranar 26 ga watan Yunin shekarar 1945. Bikin cika shekaru 80 din na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar mai wakilai 193 ke fuskantar kalubale da dama, waɗanda suka hada da makomar ta ko kuma ci gaban tasirinta baki ɗaya. Kan wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Abubakar Chika, tsohon jakadan Najeriya a Iran. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana..........
-
Aliyu Dawobe kan janyewar wasu ƙungiyoyin agaji a Arewa maso Gabashin Najeriya
25/06/2025 Duración: 03minƘungiyar agaji ta ICRC wadda ke aiki a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta bayyana damuwa da janyewar wasu ƙungiyoyin agaji da ke bai wa ƴan gudun hijira tallafi a yankin. Babban jami'in yada labaran ƙungiyar a Najeriya, Aliyu Dawobe da ke ziyarar aiki a Lagos, ya mana ƙarin bayani dangane da halin da suke ciki. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris...........
-
Janar Sani Usman Kukasheka kan rundunar tsaro ta haɗin gwiwar ƙasashen ECOWAS
24/06/2025 Duración: 03minShugabannin ƙsashen Yammacin Afrika da ke ƙarƙarshin ƙungiyar ECOWAS sun sake bayyana damuwarsu dangane da ƙruwar matsalar tsaro a yankin. Yayin taron da suka gudanar a ƙarshen mako, shugaban ƙungiyar mai barin gado kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake gabatar da buƙatarsa ta tabbatar da rundunar tsaro ta haɗin gwiwar da zata tinkari wannan matsalar. Bashir Ibrahim Idris ya tattaunawa da Janar Sani Usman Kukasheka mai ritaya,tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..........
-
Muhammad Ibrahim Sa’id kan yunƙurin kwaso ƴan Najeriya da ke Iran
23/06/2025 Duración: 03minYanzu haka ƙasashe na ci gaba da ɗaukar matakan kwashe al’ummominsu daga Iran da kuma Isra’ila, saboda yadda yaƙi ya tsananta a tsakanin ƙasashen biyu. Bayanai na nuni da cewa ofishin jakadancin Najeriya da ke Iran, ya fara tsara yadda za su kwashe ƴan Najeriya da motoci zuwa Armenia kafin wataƙila a yi amafani da jiragen don dawo su gida. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Muhammad Ibrahim Sa’id, ɗan Najeriya da ke karatu a birnin Qoom mai tazarar kilomita 150 a kudancin Tehran. Ku latsa alamar sauti domin jin zantawarsu........
-
IPMAN ta yaba wa Dangote na fara rarraba man fetur da Disal zuwa sassan ƙasar
19/06/2025 Duración: 03minƘungiyar dillalan man fatir masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN ta yaba da sabon shirin matan man Dangote na fara rarraba man fetur da Disal daga Lagos zuwa sassan ƙasar, sai dai ta ci gaba da nuna damuwa kan sabon harajin naira 12,500 da gwamnatin jihar Lagos ta sanya kan duk mota guda kafin bin titin Lekki da ke kaiwa matatar Dangote da sauran kamfanonin mai dake yankin, matakin da ya haifar da fargabar samun karin faranshin litar mai, masamman a arewacin ƙasar. Sai dai a tataunawarsa da Ahmad Abba, shugaban ƙungiyar IPMAN, Alhaji Abubakar Maigandi, ya ce bayan ɗan yajin aikin da derebobin dakon mai suka yi, gwamnatin Lagos ta sanya ranar Yau Alhamis, domin cimma matsaya kan wannan batu. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawarsu................
-
Jaloud Sambo kan juya baya ga takarar Paul Biya da ƴan adawar Kamaru suka yi
18/06/2025 Duración: 03minA yayin da guguwar siyasa ke kaɗawa a Jamhuriyar Kamaru, alamu na nuni da cewa jiga-jigan jam’iyyu da suka daɗe suna ƙawance da jam’iyyar MPRC mai mulkin ƙasar za su yi wata tafiya ta daban saɓanin ta shugaba Paul Biya ba. Bisa ga dukkannin alamu, ƙusoshin ƴan siyasa daga arewacin Kamaru da suka shafe shekaru a tafiyar kuma ke riƙe da manyan makamai irin su Isa Ciroma Bakari da Bello Buba Maigari sun fara tunanin yin watsi da tafiyar shugaba Biya, kamar yadda ake raɗe-raɗi. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Jaloud Sambo, shugaban ƴaƴan jam’iyyar adawa ta MPSC da ke zaune a ƙasashen waje.......
-
Tattaunawa da Dr Awwal Abdullahi kan kashe-kashen jihar Benue
17/06/2025 Duración: 07minShugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci jami'an tsaro da su kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar Benue ta tsakiya, inda rahotanni ke cewa fiye da mutane 200 ne suka mutu a wasu jerin hare-hare da aka kai Yelewata a baya-bayan nan. Kiran na zuwa bayan da daruruwan mutane suka gudanar da zanga-zanga a Makurdi babban birnin jihar domin nuna adawa da kashe-kashen. A tattaunarsa da Ahmed Abba, Dr. Awwal Abdullahi Aliyu, masanin harkokin tsaro, kuma babban magatakardar ƙungiyar tsoffin sojojin Najeriya, ya fara da bayyana dalilan da ke haddasa rikicin. Shiga alamar sauti domin jin cikakken bayani.....
-
Alhaji Abubakar Cika kan rikicin Isra'ila da Iran
16/06/2025 Duración: 03minA wannan litinin an shiga rana ta huɗu da fara yaƙi gadan-gadan tsakanin Isra’il ta Iran, inda kowanne daga cikin ƙsashen biyu ke amfani da manyan makamai don kai wa farmaki a kan manyan biranen ƙasashensu. Domin yin dubi a game da wannan rikici da ake ganin cewa muddun ba a dakatar da shi ba zai shafar ƙasashe da dama, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da tsohon jakadan Najeriya a Iran. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hira da Ambasada Alhaji Abubukar Cika.....
-
Farfesa Kamilu Sani Fagge kan bikin ranar dimokaraɗiyar Najeriya
12/06/2025 Duración: 03minYau Najeriya ke bikin Ranar Dimokaraɗiya, wadda gwamnatin ƙasar ta ware domin girmamawa a ranakun 12 ga watan Yunin kowace shekara, don tunawa da soke zaɓe na makamancin lokacin da gwamnatin mulkin soji ta yi a shekarar 1993. La’akari da cewa zuwa yanzu Najeriyar ta cika shekaru 26 kenan cif a ƙarƙashin mulkin Dimokaraɗiya, ya sanya Nura Ado Suleiman tattaunawa da Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawasu..............
-
Sarkin Hausawan Mokwa kan makomar al'ummar da ambaliya ta shafa
11/06/2025 Duración: 03minBayanai daga Najeriya na cewa wasu daga cikin al’ummar da ibtila’in ambaliyar garin Mokwa ta jihar Neja ya shafa sun bijirewa yunƙurin mahukunta na kwashe su daga inda lamarin ya auku.Sai dai wani jagoron al’umma a yankin ya musanta labarin, yana mai cewa jama’a a shirye suke duk lokacin da gwamnati ta shirya kwashe su. Ku latsawa alamar sauti domin jin karin bayani.....
-
Dr Mustapha Karkarna kan tanon duniya game da barazanar da Tekuna ke fuskanta
10/06/2025 Duración: 03minYayin da aka buɗe babban taro kan alkinta tekunan duniya a birnin Nice na Faransa, Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a sake rattaba hannu kan sabbin yarjejeniyoyi da za su mayar da hankali kan alkinta tekuna da kuma kare hallittun ƙarƙashin ruwa. To sai dai duk da kasancewar Nahiyar Africa yankin da yafi fama da matsalolin muhalli ciki har da gurgusowar tekun, da alama taron bai yiwa yankin tanadin komai ba. Kan haka muka tattauna da Dr Mustapha Zakari Karkarna. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Rukayya Abba Kabara................
-
Malaman makarantu sun sake tsunduma yajin aiki a Nijar
09/06/2025 Duración: 03minGamayyar ƙungiyoyin malaman makarantu da ke koyarwa a matakai daban daban a Jamhuriyar Nijar, sun sanar da shiga yajin aikin kwanki 5 a jere daga wannan litinin, tare da barazanar da baiwa kowane ɗalibi maki ɗari bisa ɗari na jarabawar da aka yi masa. Malaman suna wannan yajin aiki ne don neman gwamnati ta biya musu buƙatunsu da suka haɗa da: ɗaukar malaman kwantaragi a matsayin ma’aikata na dindindin, tare da biyan wasu kuɗaɗensu na alawus da suka maƙale a hannun gwamnati. A game da wannan batu, Ibrahim Malam Tchillo, ya zanta da shugaban ƙungiyar ASO EPT, mai fafutar samar da ilimi mai nagarta ga al’ummar Nijar wato Ibrahim Babaye Sani.Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana..................